Faransa - Coronavirus

Sama da mutane miliyan 30 sun karbi allurar rigakafin korona a Faransa

Wani dake karban allurar rigakafin korona a kasar Faransa 13 ga watan Janairun 2021
Wani dake karban allurar rigakafin korona a kasar Faransa 13 ga watan Janairun 2021 REUTERS - GONZALO FUENTES

Faransa tace kawo yanzu  ‘yan kasar sama da miliyan 30 suka karbi kason farko na allurar rigakafin COVID-19, kamar yadda hukumomin kiwon lafiya suka sanar ranar Asabar.

Talla

Tuni gwamnati na fara sassauta dokokin da ta kakaba saboda hana bazuwar cutar, inda aka bude gidajen cin abinci da shan shayi da barasa, saboda samun saukin cutar.

Ko dayake adadin mutanen da cutar da kasashe  a kasar cikin sa’o’i24 ya karu da 34, zuwa jimillar mutane dubu 83,944 tun lokacin da aka fara samun cutar.

Sassauta doka

A ranar Laraba Faransa ta shiga rukuni na 3 a kokarin sassauta dokar takaita walwalar jama’a bayan sake samun raguwar mutanen da ke kamuwa da Covid-19.

Karkashin matakan da kasar ta Turai ke bi, daga yau za ta sahale bude wasu kasuwanci da hada-hadar jama’a a yankunan da ke fuskantar dokokin takaita walwalar tsawon watanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI