Amurka - Turai

Amurka da EU sun kawo karshen rikicin jiragen samansu na shekaru 17 saboda China

Amurka da Turai sun jingine rikicin sama da shekaru 17 na jiragen samansu, ranar 15 ga watan Yuni shekarar 2021
Amurka da Turai sun jingine rikicin sama da shekaru 17 na jiragen samansu, ranar 15 ga watan Yuni shekarar 2021 AP - Francois Mori

Shugaban Amurka Joe Biden da shugabannin kungiyar kasashen Turai sun kawo karshen rikicin kasuwancin da suak kwashe shekaru 17 suna tafkawa wajen kulla yarjejeniya tsakanin kamfanin jiragen saman Boeing da AirBus.

Talla

Matakin ya biyo bayan ganawar da Biden yayi da shugabannin Turai da suka hada da Charles Michel da Ursula von der Leyen.

Tuni shugabanin bangarorin biyu suka bayyana farin cikinsu dangane da wannan gagarumin ci gaba da aka samu a kokarinsu na tinkarar kasar China, cikinsu harda Ursala Von der Leyen.

Wannan bikin ya fara da samun cigaba, akan jiragen sama. Wannan yarjejeniya tabbas ta bude sabon babi a dangantakar mu saboda mu bar bangaren shari’a a kotu zuwa hadin kai akan jiragen bayan kwashe kusan shekaru 20 ana tafka rikici. Wannan rikicin kasuwanci mafi girma a tarin kungiyar kasuswanci ta duniya.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yace, wannan yarjejeniya tsakanin kungiyar tarayyar Turai da Amurka, wanda ta kai ga cire harajin kudaden shige da fice tsakanin kasar Amurka da nahiyar babbar nasara ce, yana mai yabawa takwaransa na Amurka Joe Biden.

Tun shekarar 2004 ne Amurka da Tarayyar Turai suke takaddama a batun da suka shigar gaban kungiyar cinikayya ta duniya, a kan tallafin da Amurka ta ba kamfanin jirgin sama na kasar wato Boeing da kuma wanda EU take bai wa kamfanin Airbus na Turai.

A yanzu matsayar da suka cimma za ta ba su damar mayar da hankali a kan kalubalen da suke fuskanta daga fannin masana'antun jiragen sama na China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.