Turai-Coronavirus

Covid-19 ta ta'azzara cin hanci da rashawa a yankin Turai- Bincike

Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai.
Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai. AP - Olivier Hoslet

Kungiyar Transparency International ta ce barkewar annobar corona a duniya ta haifar da ta'azzarar cin hanci da rashawa a ilahirin kasashen nahiyar Turai, wanda ya kai ga gaza baiwa al’umma kulawar ta da dace face ga wadanda ke da alfarmar mahukunta, inda gwamnototi suka yi amfani da damar don bukatun kansu.

Talla

A binciken da ta gudanar cikin rahotanta na shekara-shekara kungiyar Transparency International mai rajin tabbatar da daidaito tare da yakar cin hanci da rashawa a duniya, ta ce ta gano karuwar rashawa da alfarma mai alaka da cin hanci a kusan daukacin kasashen Turai.

Kungiyar ta ce, ta gudanar da bincike kan sama da mutane dubu 40 a cikin kasashe mambobin EU 27 tsakanin watan Oktoba zuwa Disambar shekarar 2020, wato lokacin da annobar ta covid-19 ta tsananta a nahiyar.

Transparency ta ce binciken ya gano cewa kashi 29 cikin dari na mutanen sun dogara da neman alfarmar a alakarsu ta ‘yan uwantaka ko abokantaka kafin samun damar kulawar kiwon lafiyar da ta kamata, yayinda kashi shida daga cikin wadanda suka amsa tambayoyin suka tabbatar da bada cin hanci kai tsaye.

Binciken na Transperancy International ya bankado yadda gwamnatocin wasu kasashen na Turai ke kokarin shawo kan cutar corona ta hanyar allurar rigakafi domin wawushe biliyoyin kudade da aka ware saboda ita.

Kungiyar ta ce, matsalar cin hanci a bangaren kiwon lafiya yafi kamari a Romania da Bulgaria, yayinda neman sanin wane, yayi muni a Jamhuriyar Czech da Portigal.

Haka zalika rahoton ya ce kashi 60 na wadanda suka amsa tambayoyin kungiyar a Faransa da Poland da Spain suka ce babu haske kan yadda gwamnatocinsu ke tafiyar da yaki da annobar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI