Faransa-Sarkozy

Sarkozy ya sake gurfana gaban kotu kan badakalar yakin neman zaben 2012

Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy yayin bayyanarsa gaban kotun Paris yau talata.
Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy yayin bayyanarsa gaban kotun Paris yau talata. Christophe ARCHAMBAULT AFP

Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya musanta kashe kudaden da suka wuce kima yayin yakin neman zabensa na 2012, kalaman da ke zuwa yayin bayyanarsa gaban kotu a birnin Paris yau Talata.

Talla

Nicolas Sarkozy wanda wannan ne karo na biyu da ya ke bayyana gaban kotu cikin shekarar nan bayan gurfanarsa ta watan Maris da ya fuskanci tuhuma kan cin hanci da rashawa, ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake masa na aikata ba dai dai ba a yakin neman zaben da ya yi fatan ci gaba da zama kan madafun iko.

Sarkozy mai shekaru 66 da ke fuskantar shari’ar a kotun kasar da ke birnin Paris, masu shigar da kara na tuhumarsa da karya ka’idojin yakin neman zabe, lokacin da ya ke neman wa’adi na biyu a zaben da baiyi nasara ba, dama yadda ya samo makudan kudaden.

Ko a shari’ar watan na Maris sai da kotu ta zartaswa tsohon shugaban na Faransa hukuncin daurin shekaru 3 guda a gidan yari, biyu a gida bayan samunsa da hannu dumu dumu a badakalar rashawa, hukuncin da Sarkozy ya daukaka kara.

Sai dai Sarkozy a shari’ar ta yau, ya bayyana alkalin kotun cewa yana da cikakkiyar gogewar shekaru 40 a fannin siyasa wanda ya bashi damar lakantar hanyoyin samun kudaden yakin neman zabe ta halastacciyar hanya, a don haka babu hujjar tuhumarsa kan yadda ya samo kudaden.

Alkaluma nan una yadda Sarkozy ya kashe kudin da yawansa ya kai yuro miliyan 42 da dubu dari 8 yayin yakin neman zaben na 2012 wanda ya ki bayyana ta yadda ya samu makudan kudaden.

Yanzu haka dai kotu ta dage zaman sauraron shari’ar zuwa ranar 22 ga watan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI