Faransa-Covid-19

Za a daina sanya takunkumi a Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron cire da takunkumin fuska
Shugaban Faransa Emmanuel Macron cire da takunkumin fuska REUTERS - PHIL NOBLE

A Faransa, daga gobe Alhamis an kawo karshen yin amfani da takunkumin rufe hanci da baki a kan titunan kasar, tare da cire dokar hana fitar dare daga ranar Lahadi mai zuwa, matakan da aka dauka don yaki da cutar Covid-19.

Talla

Firaministan kasar Jean Castex ,shi ne ya sanar da hakan a ranar Laraba, saboda a cewarsa an samu gagarumar nasarar wajen yaki da wannan cuta.

Firaministan ya ce,

Za mu kawo karshen tilasta wa mutane sanya takunkumin rufe baki da hanci a waje, sai dai a wasu daidaikun wurare, kamar inda ake samun cunkoson jama’a da kuma wuraren da ala dole sai mutane sun shiga a cikin layuka, kamar kasuwanni da kuma filayen wasanni.

 

Firamistan ya kara da cewa, "Abu na gaba kuwa shi ne, dokar hana fitar dare da ke fara aiki a karfe 11 na dare, ita ma za ta kawo karshe a ranar 20 a maimakon 30 ga wannan wata kamar yadda aka sanar da farko, irin ci gban da ake samu a fannin yaki da cutar, ya nuna cewa babu hujjar da za ta sa a ci gaba da amfani da wadannan dokoki."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.