Faransa-Coronavirus

Faransa za ta fara tirsasawa jami'an lafiya karbar rigakafin covid-19

Wata mata yayin karbar allurar rigakafin covid-19 a birnin Nantes na Faransa.
Wata mata yayin karbar allurar rigakafin covid-19 a birnin Nantes na Faransa. REUTERS - STEPHANE MAHE

Faransa na shirin fara tirsasawa jami’an lafiya karbar rigakafin covid-19 karkashin shirye-shiryen daidaita al’amura bayan janye ilahirin dokokin takaita walwalar jama’a da aka sanya don yakar yaduwar cutar.

Talla

Ministan Lafiyar Faransar Olivier Veran ya ce akwai koma baya ta bangaren karbar alluran rigakafin daga jami’an lafiya idan aka kwatanta da daidaikun mutane ko da ya ke kashi 60 na jami’an sun karbi akalla allura daya ta rigakafin.

Da ya ke kira ga jami’an lafiyan musamman wadanda ke aiki a gidajen kula da tsaffi, Veran ya ce akwai bukatar su karbi dukkanin alluran biyu na rigakafin don taimakawa a yaki da cutar.

Ministan lafiyan na Faransa wanda ke batun dai dai lokacin da Faransa suka fara samun sa’idar fita waje ba tare da takunkumin rufe hanci da baki ba, ya ce za su jinkirta na dan wani lokacin don ganin yanayin raguwa ko kuma karuwar masu cutar, alkaluman da zai fayyace musu fara tirsasa karbar rigakafin.

Sai dai ministan ya ce ko a yanzu, wajibi ne ga duk wanda ke mu’amala da wuraren da za su iya haddasa masa cutar su tabbatar da karbar rigakafin.

Adadin masu kamuwa da cutar a Faransa ya ragu daga dubu 3 da ake gani a makon jiya zuwa dubu 2 inda ministan lafiyan ke cewa akwai fatan ya koma dubu guda ko kasa da haka zuwa karshen watan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI