Faransa-Coronavirus

Tarzoma ta kaure a Bretagne dake kasar Faransa

Wasu daga cikin mutanen da suka yi arrangama da jami'an tsaro a yankin Bretagne
Wasu daga cikin mutanen da suka yi arrangama da jami'an tsaro a yankin Bretagne AFP - LOIC VENANCE

A Faransa a cikin daren jiya juma’a wayewar garin yau asabar ,tarzoma ta kuno kai yayinda wasu yan sanda kusan 400 suka yi kokarin tarwatsa wasu mutane dake wani wurin shakatawa a yankin Bretagne dake yammacin kasar .

Talla

Yayin wannan arrangama, yan Sanda 5 suka samu rauni.Ana dai tuhumar mutanen ne da keta dokar ta bace dake hana fita daga karfe 11 na dare.

Tarzomar da ta kuno kai a yankin Bretagne na kasar Faransa
Tarzomar da ta kuno kai a yankin Bretagne na kasar Faransa AFP - LOIC VENANCE

A farkon makon da ta gabata ne hukumomin Faransa suka sanar da kawo karshen amfani da kyalen rufe hanci da baki a fadin kasar ta Faransa. Rahotanni daga fadar kantomar garin Redon, kusan mutane 1500 suka halarci yankin  a cikin daren jiya juma’a, wanda nan take aka soma fuskantar  rikici tsakanin jama’a, wanda hakan ya sa yan Sanda kokarin tarwatsa taron jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI