Faransa - Siyasa

Faransawa sun soma dakon sakamakon zaben yankuna

Wani mai jefa kuri'a yayin zaben shugabanni a matakin yankuna. 20/6/2021.
Wani mai jefa kuri'a yayin zaben shugabanni a matakin yankuna. 20/6/2021. REUTERS - CHRISTIAN HARTMANN

Faransawa sun kammala kada kuri’a zaben yankunan da suka yi da suka hada da manya 13 da kuma wasu kanana 96, wanda ake ganin zai zama ma’unin yadda zaben shugabancin kasar dake tafe a shekarar 2022 mai zuwa zai kaya.

Talla

Sai dai kididdiga ta nuna ba a samu fitowar jama’a sosai ba a zaben yankunan na Faransa, la’akari da cewar fiye da kashi 66 na wadanda suka cancanci kada kuri’unsu ne basu fita ba.

Ana sa ran jami’yyar RN ta jagorar ‘yan adawa a Faransar Marine Le Pen ta sake farfado da karsashinta a fagen siyasar kasar, idan har ta samu nasarar lashe zaben ko da yanki guda.

Le Pen da ta fafata da shugaban Faransa Emmanuel Macron ba za ta tsaya takara a zaben shugabancin kasar na badi ba, sai dai ta dage wajen jagorantar yakin neman zaben jam’iyyarta yayin fafatawar ta 2022, wadda kuri’ar jin ra’ayi ta nuna maiyiwuwa a tafi kankankan tsakanin jam’iyyar adawar ta RN da kuma ta shugaba mai ci La République En Marche.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI