Faransa

Macron da Le Pen sun sha kaye a zaben jihohin Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ranar 29 ga watan Matyn 2021
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ranar 29 ga watan Matyn 2021 REUTERS/Christian Hartmann/

Jam’iyar Shugaban Faransa Emmanuel Macron da ta madugun ‘yar adawa Marine Le Pen sun samu koma bayan a zagayen farko na zaben kana-nan hukumomi dake na ranar Lahadi wanda masu ra’ayin rikau ke ci gaba da samun nasara, a zaben da aka samu karancin fitowar jama’a.

Talla

Zabukan na jihohi da na kananan hukumomi na amtsayin zakaran gwajin dafi  ga zaben shugaban kasa na shekara mai zuwa – to sai dai karfe 8 na dare bayan rufe runfunar zabe, lamarin baiyiwa mahutanta a Fadar Elysee dadi ba.

Marine Le Pen ta masu tsattsauran ra'ayi da jam’iyyarta ta (RN) na fatan samun akalla mazabu 6 daga cikin manyan yankuna Mainland 13 na Faransa, to sai dai jiha daya tilo ta samu Cote d’Azur dake kudancin kasar.

Shugabar jam'iyyar masu tsattauran ra'ayi ta RN a Faransa Marine Le Pen.
Shugabar jam'iyyar masu tsattauran ra'ayi ta RN a Faransa Marine Le Pen. DENIS CHARLET AFP

Karancin fitowa

Kashi 26,72%, na wadanda suka cancanci kada kuri'u kadai suka samu fitowa zaben, wanda hakan ke nuna koma baya, idan aka kwantanta da zaben da ya gabata a shekarar 2015 da ya samu halartar kashi 40%.

Masharhanta dai sun fara bayyan fargabarsu kan matsalar da rashin halartar zaben da himma zai iya haifarawa wajen baiwa masu ra’ayin rikau nasarar lashe mafi yawan kujeru musaman a birnin Paris da kewaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI