Jamus

Dan ta'adda ya kashe mutane a birnin Wurzburg na Jamus

Motocin 'yan sanda yayin da suke kokarin isa inda wani mahari ya yi amfani da wuka wajen kashe mutane a birnin Wurzbug na kasar Jamus
Motocin 'yan sanda yayin da suke kokarin isa inda wani mahari ya yi amfani da wuka wajen kashe mutane a birnin Wurzbug na kasar Jamus © AP

Wani mahari dauke da wuka ya kashe mutane tare da jikkata wasu da dama a birnin Wurzburg dake kudancin Jamus a yau Juma’a.

Talla

Cikin sanarwar tabbatar da kai harin da ta wallafa a shafinta na Twitter, rundunar ‘yan sandan kasar ta Jamus ta ce jami’anta sun yi nasarar kama maharin bayan harbinsa da suka yi a kafa.

Sai dai kafin ya shiga hannu sai da mutumin ya halaka mutane akalla uku tare da jikkata wasu 6 a birnin na Wurzburg.

Har yanzu dai hukumomin tsaron Jamus ba su yi karin bayani kan maharin ba da kuma dalilinsa na kaiwa fararen hula farmaki.

A  shekarun baya bayan nan dai an fuskanci hare-haren kan jama’a a Jamus wadanda hukumomin tsaron kasar suka alakanta da ta’addancin masu biyayya ga kungiyoyi irinsu Al Qaeda da IS.

Hari mafi muni shi ne wanda wani mutum yayi amfani da babbar mota wajen yin tafiyar ruwa da mutane ana tsaka da bikin Kirsimeti a wata kasuwa dake birnin Berlin, abinda yayi sanadin hasarar rayukan mutane akalla 12.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.