EU - Rasha

Kuskure ne kyale wata kasa ta wakilci EU wajen ganawa da Rasha - Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. AP - John Thys

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana rashin jin dadinsa kan matakin kungiyar EU na yin watsi da kudurin hadin gwiwar Jamus da Faransa na shiga tattaunawa da shugaban Rasha Vladimir Putin domin gyara alakarsu.

Talla

Poland da wasu kasashen yankin Baltic ne suka jagoranci adawa da kudurin shiga tattaunawar da Rasha wanda Faransa da Jamus suka gabatar.

Yunkurin Emmanuel Macron da Angela Merkel dai ya biyo bayan kwarin gwiwar da suka ce sun samu daga tattaunawar da aka yi tsakanin shugaban Amurka Joe Biden da Vladimir Putin na Rasha ta ranar 16 ga watan Yuni a birnin Geneva.

Shugaban Faransa dai yayi gargadin cewa gazawa ce babba ga kasashen EU 27 su kyale wata kasa dake wajensu ta wakilce su tattaunawa da Rasha kan makomar wasu manufofi da suka shafi yankin Turai ciki har da batun takaita kera makamai ba tare da sun shiga taron kai tsaye ba.

Rabon da kasashen kungiyar EU su tattauna da Rasha tun shekarar 2014, lokacin da Rashar ta mamaye yankin Crimea na Ukraine, abinda ya gurgunta alakarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.