Amurka-Florida

Ana neman mutane 159 da suka bace bayan rugujewar bene a Amurka

Ana ci gaba da laluben baraguzan benen a Florida ko za a yi katarin samun masu sauran numfashi.
Ana ci gaba da laluben baraguzan benen a Florida ko za a yi katarin samun masu sauran numfashi. CHANDAN KHANNA AFP/File

Mutane 4 ne aka tabbatar sun `mutu a kana 159 suka bace  ya zuwa yanzu, biyo bayan rushewar wani gini na kusa da teku a kusa da gabar ruwan Miami, a yayin da masu aikin ceto ke ta kokarin lalube a baraguzan ginin, ko za su yi katarin zakulo wadanda ke da sauran shan ruwa.

Talla

A  yayin da al’ummar yankin ke cikin yanayi na tashin hankali, gwamnan jihar  Florida ya bukaci cikakken bayani a game da ummul’aba’sin wannan al’amari na rugujewar  bene mai hawa 12.

Magajiyar garin birnin, Daniella Levine Cava ta ce har yanzu hukumomi ba su kai ga samun labarin mutane 159 da watakila suna tsakiyar bacci a hasumiyar Champlain a lokacin da benen ya rushe, lamarin da ke zafafa fargabar yiwuwar karuwar adadin mamata.

Tawagar masu aikin ceto da karnuka masu shinshina na inda lamarin ya auku, suna ta lalube.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.