Rasha-coronavirus

Korona ta kashe sama da mutane 100 cikin sa'o'i 24 a Rasha

Sabon nau'in cutar korona na Delta ya hallaka sama da mutun dari a Moscou na kasar Rasha ranar 26 ga watan Yuni 2021.
Sabon nau'in cutar korona na Delta ya hallaka sama da mutun dari a Moscou na kasar Rasha ranar 26 ga watan Yuni 2021. AP - Alexander Zemlianichenko

Jami’an lafiya a Rasha sun sanar da adadi mafi yawa na mutanen da annobar Korona ta kashe a jiya Lahadi, yayin da a Indonesia, fiye da mutane dubu 21 suka kamu da cutar a rana guda.

Talla

Wannan al’amari na zuwa ne daidai lokacin da kasashen yankin Asiya da Pacific ke daukar sabbin matakan dakile yaduwar annobar Koronar dake neman sake barkewa, la’akari da karuwar adadin mutanen dake kamuwa da ita.

Kwararru dai sun danganta sabon kalubalen da ya bijiro da bullar sabon nau’in cutar Koranar daga India mai suna Delta, wanda masana suka ce shi ne mafi hatsari daga dukkanin nau’ikan cutar da suka bayyana, zalika tuni ya bazu zuwa kasashe akalla 85 a yanzu haka.

A mafi akasarin kasashen Turai da Amurka al’amura sun soma daidaita bayan raguwar kaifin cutar bayan yiwa miliyoyin mutane alluran rigakafi, sai dai a Rasha lamarin ya sha banban, inda a jiya lahadi kadai, annobar ta lakume rayukan mutane 144, adadi mafi yawa da aka gani a gasar.

A kudancin nahiyar Asiya da Australia ma dai sabon nau’in Koronar na Delta na cigaba yaduwa, abinda ya tilastawa mutane akalla miliyan 5 sake komawa karkashin dokar kullen makwanni 2 a birnin Sydney, yayin da kuma a Indonesia fiye da mutane dubu 21 suka kamu da cutar a rana 1, adadi mafi yawa da aka gani a kasar.

Kawo yanzu mutane kusan miliyan 4 annobar Korona ta halaka a fadin duniya, tun bayan bullarta daga birnin Wuhan na kasar China a Disambar shekarar 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.