Birtaniya - Coronavirus

Ministan lafiyar Birtaniya yayi murabus saboda karya dokokin yaki da Korona

Ministan lafiyar Birtaniya Matt Hancock.
Ministan lafiyar Birtaniya Matt Hancock. Tolga Akmen AFP/Archivos

Ministan Lafiyar Birtaniya Matt Hancock ya ajiye aikinsa a yau Asabar, bayan samunsa da laifin karya dokokin dakile yaduwar annobar Korona, a yayin da yake lalata da wata ma’aikaciyarsa da ta kasance matar aure.

Talla

‘Yan adawa a Birtaniya dai sun dade suna zargin gwamnatin kasar da munafurci dangane da karya dokokin yaki da annobar Korona da suka ce suna yi da gangan a lokacin da suke umartar jama’a da su kiyaye su.

Hancock ya sanar da matakinsa na yin murabus ne cikin wasikar da ya aikewa Firaministan Birtaniya Boris Johnson a yau Asabar.

Ministan lafiyar na Birtaniya ya amince da cewar ya baiwa al’ummarsa kunya ne bayan da jaridar The Sun da ake wallafata a Birtaniya, ta wallafa wani hoton da Kemara ta dauka a yayinda yake sumbatar wata ma’aikaciyarsa a cikin ofishinsa ranar 6 ga watan Mayu.

Matt Hancock da ma’aikaciyar tasa dai dukkaninsu na da aure, kuma bayanai sun ce sun fara haduwa da juna ne tun a jami’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.