Zaben Faransa

Le Pen ta kasa samun jiha guda a zaben Faransa

This combination of file pictures showsFrench presidential election candidate for the En Marche ! movement Emmanuel Shugaban Faransa Emmanuel Macron da babbar abokiyar hamayyarsa Marie Le Pen
This combination of file pictures showsFrench presidential election candidate for the En Marche ! movement Emmanuel Shugaban Faransa Emmanuel Macron da babbar abokiyar hamayyarsa Marie Le Pen MIGUEL MEDINA, Eric FEFERBERG / AFP

Jam’iyyar masu tsatsauran ra’ayi a Faransa ta Marine Le Pen ta gaza samar da iko a jiha guda a zagaye na biyu na zaben yankuna da kananan hukumomi da aka gudanar jiya Lahadi, yayin da jam’iyya mai mulki ta shugaba Emmanuel Macron ta sake fuskantar koma baya kamar yadda lamarin ya kasance a zagayen farko na zaben.

Talla

A wani mataki dake tabbatar da abubuwan da suka wakana a zagayen farko na zaben jihohi da na kananan hukumomi na ranar 20 ga watan Yuli da muke ciki, sakamakon zabukan da ke fitowa daga Faransa sun  nuna yadda Marine Le Pen dake zama babbar abokiyar hamayyar shugaba Macron da jam’iyyarta ta RN suka gaza cimma burinsu na samun nasara a jihar Provence Alpes-Cote d'Azur mai dauke da Marseille da  Nice.

Yayin da shugaba Macron dake neman sake zaben sa a shekarar 2022 a wani sabon wa’adi da Jam’iyyar sa mai mulki ta Repuplique en Marche suka fuskanci mummunar koma baya.

Le Pen ta nuna burin ta na samun nasara a yankin dake gabar tekun Mediterraniya mai dauke da manyan yankuna 13, wajen kara mata kaimin kalubalantar Macron a zaben shugaban kasa, amma sai ta rasa wannan damar.

Da take mayar da martani akan sakamakon zaben bayan shan kaye Marine Le Pen ta alakanta lamarin da karincin fitowar masu kada kuri’u da kuma rashin kawance na gari tsakaninta da sauran jam’iyyun adawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.