Faransa-Auren jinsi

Faransa ta halasta yiwa masu auren jinsin dashen 'ya'ya don samun zuriya

Wasu masu ra'ayi da dabi'ar auren jinsi yayin gangami a birnin Warsaw na kasar Poland.
Wasu masu ra'ayi da dabi'ar auren jinsi yayin gangami a birnin Warsaw na kasar Poland. REUTERS - KACPER PEMPEL

Majalisar dokokin Faransa ta amince da dokar da ke bai wa masu auren jinsa da kuma matan da ba su da aure damar samun kulawa daga jami’an kiwon lafiya domin samun ‘yaya kamar dai yadda sauran ma’aurata daga jinsin mace da namji ke da irin wannan damar.

Talla

An dai share tsawon shekaru biyu ‘yan majalisar dokokin na tafka mahawara game da wannan doka, inda ‘yan majalisa 326 suka amince da ita, 115 suka nuna rashin amincewa yayin da 42 su ka yi rowar kuri’unsu.

Kafin amincewa da wannan doka, masu zamantakewar aure ta tsakanin miji da mata ne kawai ke da damar samun taimakon likita wajen neman haihuwa, ta hanyar yi wa macen dashen maniyyi, yayin da masu auren jinsi, da kuma mata marasa aure da ke neman ‘yaya sai dai su yi balaguro zuwa kasashen waje kafin su samu biyan bukata.

Wannan sauyin zai saka Faransa a jerin kasashen Turai da dama ciki har da Belgium, Netherlands, Sweden da kuma Spain da masu auren jinsi daya ke da irin wannan dama ta samun kulawar jami’an kiwon lafiya wajen dashen 'ya'ya.

Tun a shekarar 2017 ne shugaba Emmanuel Macron ya yi alkawarin cewa sai an kafa wannan doka a Faransa, domin bai wa mata biyu da ke auren juna ko kuma macen da ba ta da auren damar samun ‘ya'ya a rayuwarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.