TURAI - IFTILA'I

Kakkarfar Guguwa ta tafka barna a kasashen Faransa, Jamus da Switzerland

Guguwa ta tafka barna a kudancin Jamus, 29 ga watan Yuni 2021.
Guguwa ta tafka barna a kudancin Jamus, 29 ga watan Yuni 2021. Christoph Schmidt dpa/AFP

Ruwan sama da iska mai karfin gaske gami da kankara sun afka wa kasashen Turai da dama da suka hada da Jamus, Switzerland da kuma Faransa, lamarin da ya yi sanadiyyar ambaliya da kuma haddasa barna mai tarin yawa a wadannan kasashe.

Talla

Ruwan da kuma iskar sun kwashe rufin gidaje tare da toshe hanyoyin mota lamarin da ya tilasta wa mahukunta daukar matakin dakatar zirga-zirgar jiragen kasa a birnin Stuttgart da ke kasar Jamus.

Hotunan bidiyo sun nuna yadda koguna da kananan koramu da dama suka cika makil, sai kuma manyan bishiyoyi da suka datse hanyoyi, kamar dai yada ake ganin motoci da dama na yawo kan ruwa a mafi yawan yankunan kasar ta Jamus.

A kasar Switzerland kankarar da ke sauka ce ta yi mummunan ta’adi ga gidaje da kuma motoci musamman ma a yankin Notwill, yayin da jami’an agaji suka kai wa mutane akalla 16 dauki bayan da suka makale a cikin gidajensu.

An samu irin wannan ambaliya da saukar kankara a kudu maso gabashin Faransa, kuma tuni hukumar kula da hasashen yanayi ta fitar da gargadi dangane da yiyuwar samun irin hakan a wasu jihohi da ke arewa maso gabashin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.