faransa - Yanayi

Kotun Faransa ta baiwa gwamnati wa'adi don cimma muradun sauyin yanayi

Hayaki mai gurbata muhalli a kasar China.
Hayaki mai gurbata muhalli a kasar China. AP - Sam McNeil

Kotun kolin Faransa ta bai wa gwamnatin kasar wa’adin watannni 9 ta dauki dukkannin matakan da suka dace wajen cimma muradanta a kan sauyin yanayi ko kuma ta fuskanci hukunci.

Talla

Hukuncin da aka yanke biyo bayan karar da garin Grande-Synthe, da ke gabar tekun arewacin kasar Faransa ya shigar, kotu ta umurci Firaminista Jean Castex ya dauki dukkanin matakan da suka dace na kawar da hayakin da ke illata muhalli zuwa ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2022,  ko kuma a ci ta tara mai nauyi.

Wannan wa’adi ya zo daidai da makonnin karshe na yakin neman zaben shugaban kasa a Faransa, kuma abin da hakan ke nufi shine, shugaba Emmanuel Macron, wanda ake sa ran zai nemi wa’adi na 2 zai sha kalubale a kan batun da shine babban maudu’i a zaben.

Faransa, wacce ta karbi ragamar shugabancin kungiyar Tarayyar Turai a watan Janairu, tana kokarin bijirowa da sabuwar dokar da za ta tsaurara matakan hana masana’antu, da bangaren sufuri fitar da hayaki mai gurbata yanayi.

Duk da alkawarin da ya yi a shekarar 2017 na maido da martabar muhalli, shugaba Macron ya sha fuskantar suka dangane da gaza cimma mradan da kasar ta kudiri aniyar cimma, a karkashin yarjejeniyar sauyin yanayi na Paris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.