Faransa-Zaben Faransa

Faransa ta tsayar da ranar zaben shugaban kasa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron AP - Sarah Meyssonnier

Hukumomi a Farsansa sun sanar da ranar 10 ga watan Afrilu a matsayin ranar da za a kada kuri’ar zaben shugaban kasa zagaye na farko a kasar.

Talla

Haka kuma an tsayar da ranar 24 ga watan na Afrilun dai, a matsayin ranar da za a kada kuri’a zagaye na biyu kamar yadda jami’in yada labaran gwamnatin kasar Gabriel Attal ya bayyana wa manema labarai.

Kazalika an tsayar da ranar 12 da kuma 19 a matsayin ranakun da za a gudanar da zabubbukan ‘yan majalisa.

Bisa al’ada, shugabannin kasa da aka zaba a Faransa na shafe shekaru 5 kan karagar mulki, a zaben da ake kada shi karkashin tsarin zagaye biyu.

A zaben baya da ya gabata, shugaban kasar na yanzu Emmanuel Macron ya kada abokiyar karawarsa, 'yar gwagwarmayar kwato hakkin dan adam Marine Le Pen.

Har yanzu, shugaba Macron bai bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a karo na biyu a hukumance ba, amma dai duk alamu sun nuna cewa zai tsaya din.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.