Faransa - Google

Faransa taci tarar Google Euro miliyan 500

Logon kamfanin sadarwa a yanar gizo Google.
Logon kamfanin sadarwa a yanar gizo Google. Lionel BONAVENTURE AFP/Archivos

Hukumar Kula da fasahar jama’a a Faransa taci tarra kamfanin Google euro miliyan 500 saboda samun sa da laifin sanya labaran kamfanonin Faransa ba tare da karbar izinin su ba kamar yadda dokokin turai suka tanada.

Talla

Shugabar Hukumar Isabelle De Silva ta shaidawa manema labarai cewar wannan itace tarar mafi girma da aka dorawa wani kamfani saboda kin mutunta dokokin hukumar.

Hukumar ta kuma bukaci Google ya biya kamfanonin labaran saboda amfani da labaran su, ko kuma ya fuskanci biyan diyyar euro dubu 900 kowacce rana.

Ko a bayan saida Faransa ta ci kamfanin Google tarar Euro miliyan 50 sakamakon samun kamfanin da laifin kin bayar da haske a cikin ayyukan da yake gudanarwa a kasar, kamar dai yadda ka’idojin kungiyar Turai suka tanada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.