Faransa - Shari'a

Ministan shari'ar Faransa ya gurfana gaban kotu

Ministan shari’ar Faransa Eric Dupond-Moretti. 6/7/2021.
Ministan shari’ar Faransa Eric Dupond-Moretti. 6/7/2021. © AFP/Bertrand Guay

Alkalan Faransa na tuhumar Ministan shari’ar kasar Eric Dupond-Moretti bisa zarginsa da yin amfani da karfin mukaminsa wajen aikata ba daidai ba.

Talla

Eric Dupond-Moretti, da yayi fice a aikin lauya wanda kuma shugaba Emmanuel Macron ya nada shi kan mukamin ministan Shari’ar Faransa a shekarar bara, ya gurfana gaban kotu a yau Juma’a ne bisa tuhumar amfani da matsayinsa wajen yin ramuwar gayya kan abokan aikinsa masu adawa da shi a tsawon lokacin da ya shafe yana aikin lauya a shekarun baya.

Eric Dupond ne Ministan shari’ar Faransa na farko da aka gurfanar da shi a gaban shari’a, matakin da ya bayyana a matsayin bita da kullin wani gungun ma’aikatan shari’a dake hankoron ganin ya rasa mukaminsa.

Bayanai dai sun ce a wani abin da ba a saba gani ba, masu bincike sun shafe awanni 15 suna laluben ofishin ministan shari’ar na Faransa yayin neman hujjojin tabbatar da tuhumar da ake masa.

Sai dai Firaministan Faransa Jean Castex ya kare Dupond-Moretti daga zargin da ake masa, tare da bayyana ci gaba da goyon bayan ministan dari bisa dari kan shirinsa na yin garambawul ga wasu tsare-tsaren shari’ar Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.