Faransa-Marseille

Gobara ta kashe 'yan cirani 3 a Marseille

Jami'an kwana-kwana a gaban ginin da gobara ta yi sanadin mutuwar mutane 3 a Marseille.
Jami'an kwana-kwana a gaban ginin da gobara ta yi sanadin mutuwar mutane 3 a Marseille. © AFP

Hukumomi sun ce mutane 3 sun mutu a birnin Marseille da ke kudancin Faransa a yau Asabar, a yayin da gfobara ta tashi a wani bene da ake zaman haya.

Talla

Wani yaro  mai shekaru 2 da wani mutum sun samu mummunan rauni a gabarar data kama ginin da akasari baki ‘yan Najeriya ke zaune a ciki, kuma majiyoyin bangaren shari’a sun ce mutane ukun da suka mutu bakin haure ne wadanda ba su da rajista.

Babban jami’in ‘yan sanda, Frederique Camilleri ya ce ba  a kai ga tantance ainihin musabbabin wannan gobara, wadda ta tashi daga hanyar da wayoyin wutar lantarki suka bi ba.

Hukumomi na kokarin samar wa da wadanda suka tsira daga wanna gobara matsuguni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.