Birtaniya - Korona

Birtaniya ta sassauta dokokin hana yaduwar cutar korona a Ingila

An saukaka dokokin hana yaduwar cutar korona a ingila, Litinin 19 ga watan Yuli 2021.
An saukaka dokokin hana yaduwar cutar korona a ingila, Litinin 19 ga watan Yuli 2021. Tolga Akmen AFP

Hukumomi Britaniya sun dage tsauraran matakan kariya daga annobar Coronavirus a Ingila, duk da cewa masana  da ‘yan adawa na ganin dage matakan na da hadarin gaske a halinda ake ciki.

Talla

Tun daga Littinin din nan Hukumomin kasar suka bada izinin a bude wuraren shakatawa kuma wuraren taruwan mutane a hada yawan mutane da aka ga dama sannan kuma ana iya daina amfani da kyallen rufe baki da hanci, da hana jama’a aiki daga gida da aka kafa a chan baya.

Franministan Birtaniya  Boris Johnson wanda shi kansa saida ya kebe kansa, ya nemi jama’a da a kiyaye kuma a tabbatar cewa an karbi alluran rigakafi da aka samar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.