Faransa - Coronavirus

Masu shiga Faransa daga Turai zasu gabatar da sabuwar shaidar gwajin korona

Fasinjoji a filin tashi da saukar jiragen saman Faransa na Roissy Charles de Gaulle dake Paris
Fasinjoji a filin tashi da saukar jiragen saman Faransa na Roissy Charles de Gaulle dake Paris © AFP/Ian Langsdon

Faransa ta ce daga yanzu za ta bukaci baki daga wasu kasashen Turai da su nuna shaidar gwajin da ke tabbatar cewa, ba sa dauke da cutar Korona, kuma tilas ne gwajin ya kasance an yi sa da akalla sa’o’i 24  kafin ziyartarsu kasar.

Talla

Firaministan Faransa Jean Castex ya ce, kasashen da wannan doka ta shafa sun hada da Birtaniya, Spain, Portugal, Cyprus, Girka da Netherlands kuma tuni dokar ta fara aiki a karshen mako.

Kodayake Firaministan ya ce, bakin da suka karbi rigakafin da Hukumar Tantance Magunguna ta Turai ta amince da su kamar Pfizer da BioNTech da Moderna da Astrazaneca ko kuma Johson and Johnson, ba za a takura musu ba wajen nuna shaidar gwajin cutar.

A bangare guda, Faransar ta sanya Tunisia da Mozambique da Cuba da Indonesia cikin jerin kasashe masu fuskantar hatsarin annobar Korona.

Larura mai tsanani ce kawai za ta sa a Faransa ta amince ‘yan asalin wadannan kasashe su shiga cikin kasarta kuma da sharadin cewa, sai sun killace kansu na tsawon kwanai bakwai da zarar sun shiga kasar tare da cewa, an yi musu rigakafin cutar.

Sabon mtakin na Gwamnatin Faransa na zuwa ne a daidai lokacin da akasarin kasashen Turai ke yaki da tsanantar annobar, musamman ma bayan bullar sabon nau’in cutar da ake kira Delta mai saurin yaduwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.