Faransa - Coronavirus

Faransawa na adawa da sabbin dokokin korona dake takaita walwala

Masu zanga-zangar adawa da dokokin korona a Faransa, 21 ga watan Yuli 2021.
Masu zanga-zangar adawa da dokokin korona a Faransa, 21 ga watan Yuli 2021. REUTERS - GONZALO FUENTES

Sabbin ka’idojin zirga-zirgar mutane za su fara aiki a kasar Faransa domin bawa mutane damar ziyartar wuraren taron jama'a yayin da ake kokarin shawo kan annobar Covid-19. Sabuwar dokar ta ce daga wannan Laraba, an bawa masu shaidar rigakafi ko kuma wadanda gwaji ya tabbatar basa dauke da cutar, damar ziyarar gidan adana kayan tarihi da gidajen kallo hadi da sauran wuraren shakatawa.

Talla

Ana sa ran majalisar dokokin kasar za ta yanke shawarar ko dokar za ta iya shafar shaguna da wuraren cin abinci da bangaren tafiye-tafiyen jama’a, lamarinda ya fusata wasu ‘yan kasar, inda wasu ‘yan majalisu suka fuskanci barazanar kisa gabanin fara zaman majalisar.

Da dama daga cikin al’ummar kasar dai na bayyana hakan a matsayin kama karya a bangaren kiwon lafiya, inda suke kallon matakin da cewa yunkuri ne na shiga hakkin jama’a

Abin da bayanai ke cewa shine, idan har gwamnati ta samu nasarar aiwatar da wannan doka, shakka babu wadanda basu da shaidar rigakafi ko kuma ake wasi-wasi game da lafiyar su, to kuwa batun shiga jirgin kasa babu, bare shiga wuraren shan shayi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa mutum dubu goma sha takwas ne suka harbu da cutar korona cikin sa’o’i ashirin da hudu a kasar Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.