Bakin haure

Bakin haure 45 sun nutse a tekun Girka

An yi nasarar ceto wasu daga cikin bakin da suka nutse a tekun na Girka
An yi nasarar ceto wasu daga cikin bakin da suka nutse a tekun na Girka AFP - FADEL SENNA

Wani jirgi dauke da bakin haure 45 ya nutse a tekun Girka a lokacin da suke kokarin tsallakawa nahiyar Turai, kuma a yanzu haka mutum sama da 12 ne ake ci gaba da laluben inda ruwa ya kai su.

Talla

Jami’an tsaron gabar kogin Girka tare da Ma’aikatar Tsaro ta Turkiyya suka ce tuni aka baza jami’ai domin ceto bakin hauren.

Bayanai sun ce bakin haure 37 ne, wadanda akasarinsu sun fito ne daga kasashen Syria da Iraqi aka samu nasarar cetowa yanzu haka, inda ake laluben sauran wadanda suka nitse a ruwan.

Mutum biyar ne masu aikin ceto suka gano ta hanyar amfani da wani jirgin mai saukar Ungulu a wani tsibirin Girka da yammacin ranar Alhamis, inda aka gano sauran mutum 30 din , ciki har da mata da yara a kudu maso gabashin gabar kogin.

Tuni Jami’an tsaron gabar tekun Turkiyya suka fara bincike, bayan da suka samu bayanan inda jirgin ya nutse,, wanda tazarar kilomita 260 ne tsakanin wurin da wani wurin shakatawa na Kas da ke kudu maso yammacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.