Faransa-Coronavirus

Faransa ta bullo da sabuwar dokar yaki da Korona

Zauren Majalisar Dokokin Faransa
Zauren Majalisar Dokokin Faransa AP - Michel Euler

‘Yan Majalisar Dokokin Faransa sun kada kuri’ar amicewa da wani kudirin dokar yaki da cutar Korona wanda zai tilasta wa daukacin ma’aikatan lafiyar kasar karbar allurar rigakafin annobar.

Talla

‘Yan Majalisar sun amince da kudirin dokar ne bayan shafe tsawon kwanaki suna tafka muhawara kuma sun dauki matakin ne domin hana yaduwar sabon nau’in Korona da ake kira Delta.

Mambobin majalisar sun kada kuri’ar ce cikin nishadi da annashuwa, inda 117 daga cikinsu suka amince da dokar, yayin da 86 suka nuna turjiya.

Kodayake wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewa, da dama daga cikin Faransawa na adawa da wannan doka saboda tsaurinta a ganinsu.

Karkashin sabon matakin na yaki da cutar Korona, za a tilasta wa ma’aikan jinya da wasu kwararru a bangaren kiwon lafiya karbar rigakafin annobar.

Kazalika dole ne ma’aikatan da ke kula da wuraren taruwar jama irinsu Sinima da gidajen abinci su karbi cikakken rigakafin annobar kamar yadda kudin dokar ya fayyace.

Duk kuwa wanda ya ki mutunta wannan sabuwar doka, za a dakatar da biyan sa albashi, sannan daga bisani a sallame shi daga bakin aiki muddin ya shafe wa’adin watanni biyu ba tare da mika wuya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.