Australia-zanga-zanga

An yi arangama tsakanin 'yan sanda da masu adawa da kulle a Australia

Mutane da dama ne aka kama a yayin zanga-zangar adawa da kulle a Australia.
Mutane da dama ne aka kama a yayin zanga-zangar adawa da kulle a Australia. Steven SAPHORE AFP

Dubban mutane ne suka yi tattaki a birni na biyu mafi girma a Australia a wata zanga zangar adawa da dokar kulle a yau Asabar, lamarin da ya janyo arangama da ‘yan sanda a birnin Sydney.

Talla

An kama gwamman mutane bayan  zanga-zangar  da suka gudanar ba bisa ka’ida ba  ya saba dokokin kiyaye  lafiya a birnin Sydney, a yayin da aka yi ta dauki-ba-dadi da ‘yan sanda yayin gangamin da aka shafe sa’o’i ana yi.

An yi ta jifan jami’an tsaro da tukwanen furanni da kwalaben ruwa a yayin da masu adawa da dokar zama  a gida don dakile yaduwar annobar Covid-19 da ta shafe watanni tana aiki a birnin suka bazama tituna.

Zalika, dubban masu zanga- zanga sun taru a tituna da daman a birnin Melbourne bayan wani taro  a wajen ginin majalisar dokokin jihar a tsakar ranar wannan Asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.