Faransa-Japan

Macron ya buge da ganawa da takwaransa na Japan daga kallon bude Olympics

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. Koji Sasahara/Pool via REUTERS

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gana da takwaransa na Japan a yau Asabar jim kadan bayan da ya kalli bikin bude gasar wasannin motsa jiki na Olympics da aka yi a birnin Tokyo.

Talla

Macron yana birnin Tokyo ne don hallartar gasar wasannin bazarar da aka jinkirta da shekara  daya kuma an tsaida cewa za a gudanar da gasar  wasanni ta 2024 a birnin Paris.

Yana daya daga cikin kimanin jami’ai dubu daya, ciki har da uwargidar shugaban Amurka Jill Biden da suka halarci bikin bude gasar wasannin a ranar Juma’a.

An takaita ‘yann kallon da za su shiga kallon wasanni don rage yaduwar Korona virus duba da yadda ake samun hauhawar masu kamuwa da cutar a birnin, lamarin da ya tilasta ake akasarin wasannin ba tare da ‘yan kallo ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.