Faransa - Addini

Majalisar Faransa ta amince da kudirin dokar yaki da tsatsauran ra'ayin Islama

Shugaban Faransa Emmanuel Macron 23-07-21
Shugaban Faransa Emmanuel Macron 23-07-21 Daniel Cole POOL/AFP/File

Majalisar dokokin Faransa ta amince da wani kudirin doka mai cike da cece-kuce duk da kakkausar suka daga bangaren ‘yan majalisun jam’iyyun adawa.

Talla

Gwamnatin shugaba Emmanuel Macron ta yi ikirarin cewa ana bukatar dokar ne domin karfafa tsarin gudanar da addini a Faransa, to sai dai masu suka na cewa matakin keta ‘yancin addini ne.

Bayan muhawara ta tsawon watanni bakwai  da akayi ta kai ruwa rana tsakanin bangarorin siyasar kasar, daga karshe ‘yan majalisu 49 suka amince da dokar yayin da 19 suka ki amincewa, sai kuma wasu biyar sukayi rowan kuri’unsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.