Turkiya - Kurdawa

An kashe sojojin Turkiya biyu a yankin Kurdawa na Syria

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan, 20 - 07 -21.
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan, 20 - 07 -21. AP - Nedim Enginsoy

An kashe sojojin Turkiya biyu tare da jikkata wasu biyu a wasu yankunan arewacin Siriya da ke karkashin ikon Ankara inda take fatattakar mahara masu ikirarin jihadi da ‘yan tawayen Kurdawa.

Talla

Ma'aikatar tsaron Turkiya ta ce "'yan ta'adda" sun farmaki wata motar sojan Turkiyya ne a ranar Asabar a wani yankin dake kuduncin iyakar Syria, sai dai ba ta fayyace kungiyar da taka harin ba.

Turkiyya ta kaddamar farmaki a shekarar 2016 domin fatattakar masu dauke da makamai dake da'awar kafa daular Islama da sojojin sa kai na Kurdawan Siriya da Ankara ke daukar su amatsayin "yan ta'adda daga iyakarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.