Faransa-Coronavirus

Faransa ta amince da sabuwar dokar Korona

Zauren Majalisar Dokokin Faransa
Zauren Majalisar Dokokin Faransa AFP - THOMAS SAMSON

‘Yan majalisar Faransa sun amince da dokar da ke tilasta wa jama’a nuna shaidar cewa an yi masu rigakafin Covid-19 kafin samun damar shiga filayen wasanni da gidajen barasa da na sinima, duk da cewa dubban mutane sun gudanar da tarzomar kin amincewa da hakan a karshen makon da ya gabata.

Talla

‘Yan majalisar sun kada kuri’ar amincewa da wannan dokar ce a yammacin ranar Lahadi bayan share tsawon kwanaki suna tafka maharawa a game da kudurin da za a iya cewa raba kawunan al’ummar kasar ne.

‘Yan majalisar dokoki 156 ne suka amince da dokar, 60 suka nuna rashin amincewa da ita, sai wasu 14 da suka yi rowar kuri’unsu, yayin da daya daga cikin masu adawa da gwamnatin da ke karagar mulkin kasar Jean-Luc Melenchon ya bayyana dokar a matsayin wadda ta yi hannun riga da kundin tsarin mulkin kasar.

Wasu daga cikin abubuwan da ke kunshe a dokar sun hada da tilasta nuna katin shaidar an yi wa mutum rigakafin Korona kafin shiga wuraren taruwar jama’a, da suka hada da tashoshin mota da gidajen cin abinci da na baraza da sinima har ma da na wasan kwaikwayo.

To sai dai ‘yan majalisar sun ki amincewa da wani bangare na daftarin dokar da ke neman a kori wanda ya ki amincewa a yi masa rigakafin korona daga aiki, a maimakon haka za dakatar da albashinsa ne har sai ranar da ya nuna cewa ya yi allurar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.