Turai-Coronavirus-Zanga-zanga

Sama da mutane dubu 100 sun yi zanga-zagar adawa da dokokin Korona a Turai

Masu zanga zanga da kyalen rufe baki da hanci a Jamus.
Masu zanga zanga da kyalen rufe baki da hanci a Jamus. AFP

Sama da mutane dubu 100 sun gudanar da zanga-zanga a Australia da Faransa da Italiya da kuma Girka domin nuna adawa da sabbin tsauraran matakan yaki da cutar Korona da gwamnatocin kasashensu suka gabatar a baya-bayan nan.

Talla

Masu zanga-zangar sun yi arangama da jami’an ‘yan sanda, yayin da aka cafke da dama daga cikinsu musamman a birnin Sydney, inda shugaban ‘yan sandan yankin ya bayyana masu boren a matsayin sakarkaru bayan sun yi ta jefe-jefe da karikitai.

A Faransa kuwa, jami’an ‘yan sandan sun cilla hayaki mai sa kwalla da kuma watsa ruwan zafi don tarwatsa masu zanga-zangar da adadinsu ya kai dubu 160 a sassan kasar.

Faransawan dai  sun nuna adawarsu karara ga matakan kiwon lafiya da shugaba Emmanuel Macron ya amince da su ciki kuwa har da takaita yawan masu shiga gidajen cin abinci da sauran wuraren shakatawa musamman ma ga mutanen da ba su karbi rigakafin cutar Korona ba.

Sai dai a Indonesia da Birtaniya, gwamnatocin kasashen biyu sun ci gaba da sassauta  matakan yaki da annobar duk da cewa tana tsananta tare da yaduwa.

A can birnin Athens na Girka kuwa, an samu akalla mutane dubu 5 da suka yi tattaki dauke da alluna masu mabanbantan sakwanni ciki kuwa har da mai cewa, “ Kar ku taba mana ‘ya’yanmu.

Haka ma a Italiya, masu irin wannan zanga-zangar sun taru a birnin Rome domin nuna rashin amincewa da dokar tilasta gudanar da bukuwan nishadi da cin abincin dare a cikin gida..

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.