Faransa-Polynesia

Ana dakon jawabin Macron kan wata badakala a Polynesia

Shugaban Faransa Emmanuel Macron a tsibirin Polynesia
Shugaban Faransa Emmanuel Macron a tsibirin Polynesia AFP - LUDOVIC MARIN

Ana dakon jawabin shugaban Faransa Emmanuel Macron da ke ziyara a tsibirin Polynesia, game da batun badakalar rashin lafiyar da mutanen yankin ke fama da shi wanda ya samo asali a dalilin gwaje-gwajen nukiliya da Faransar ta yi a yankin shekaru 40 da suka gabata.

Talla

Bayan da ya baro birnin Tokyo na kasar Japan inda ya halarci bikin buda wasannin Olympics, shugaba Macron ya samu tarba ta musamman  daga mutan tsibirin, yayin da kananan yara suka yi masa lale marhabin, sannan suka sanar da shi cewa  al’ummar Polynesia na jiran furucinsa cike da kyakywan fata kan badakalar nukiliyar.

Wannan ziyara, ita ce irinta ta farko da shugaba Macron ya kai tsibirin na Polynisia da ke kudancin tekun Pacific mai fadin nahiyar Turai, bayan da ya soke  ziyarar farko da ya yi niyar kai wa yankin a 2020 saboda tsannatar annobar Covid 19.

Ina son in gabatar da wani muhimmin sako mai karfi, domin yin kira "ga kowa da kowa, mata da maza da su yi allurar rigakafin hana kamuwa da annobar Korona, domin ana kamuwa da ita ta ko wacce hanya, idan an yi allurar, to mun tsira daga kamuwa da cutar, kuma ba za mu iya yadata ba"   in ji shugaba Macron

Ya zuwa yanzu, shugaban na Faransa bai ce uffam ba game da badakalar ta gwajin nukiliyar, illa janyo hankalin mazauna tsibirin da su kare kansu daga kamuwa da cutar Korona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.