Isra'ila - Faransa

Ministan tsaron Isra’ila na ziyara a Faransa game da leken sirrin Pegasus

Ministan tsaron Isra'ila  Benny Gantz.
Ministan tsaron Isra'ila Benny Gantz. Emmanuel DUNAND AFP/File

A wannan Litinin ministan tsaron Isra’ila Benny Gantz na ganawa da takwarar aikinsa ta Faransa Florence Parly a birnin Paris daidai lokacin da bayanai ke cewa an yi amfani da manhajar Pegasus da kamfanin NSO na Isra’ila ya kera don leken asirin ‘yan jaridu da shugabannin duniya ciki har da Emmanuel Macron.

Talla

Kafin wannan ziyara ta Gantz, tuni shugaba Macron ya zanta ta wayar tarho da firaministan Isra’ila Naftali Bennett, inda bayanai ke cewa mutanen biyu sun tabo wannan batu na bibiyar wayoyin jama’a a asirce.

Ministan tsaron na Isra’ila zai sanar da mahukuntan Faransa karin bayani a game da ka’idojin sayarwa da kuma yin amfani da manhajar ta Pegasus, tare da kokarin hana samun sabani tsakanin kasashen biyu bayan da aka ruwaito cewa layin wayar da Macron ke amfani da shi tun 2017 na daga cikin lambobin wayoyi sama da dubu 50 da ake bibiya a asirce.

Tuni dai gwamnatin Isra’ila ta sanar da kafa kwamitin da zai binciki wannan zargi, tare da gano ko wadanda aka sayar wa wannan manhaja ta Pegasus na amfani da ita kamar yadda ka’idoji suka shata.

Ita ma dai majalisar dokokin Isra’ila Knesset, ta kafa nata kwamiti don binciken wannan batu, tare da tabbatar da cewa kasashen da aka sayar wa Pegasus ba su ketare ka’idojin amfani da shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.