Amurka

Miliyoyin Amurkawa na fuskantar gamuwa da fushin masu gidan haya

Shugaban Amurka Joe BIden.
Shugaban Amurka Joe BIden. AP - Susan Walsh

Miliyoyin Amurkawa na fuskantar hadarin kasancewa babu muhallai, a yayin da dokar nan da ta dakatar da masu gidajen haya daga korar masu haya ke daina aiki, a daidai lokacin da annobar coronavirus ke dada kamari, a tsakankanin cece-kucen siyasa.

Talla

A yayin da har yanzu ba a kai ga yin  amfani da biliyoyin daloli na kudaden gwamnati da aka ware don taimaka wa masu zama a gidajen haya ba, a wannan mako shugaba Joe Biden ya bukaci majalisar dokokin kasar ta tsawaita dokar da ta sahale daga wa masu haya kafa, bayan da wani hukuncin kotun koli ke nuni da cewa gwamnatin kasar ba ta da hurumin yin haka.

Amma ‘yan jam’iyyar  Republican sun yi watsi da yunkurin Democrat na tsawaita dokar zuwa tsakiyar watan Oktoba, kuma majalisar wakilan kasar ta dage zaman ta don tafiya hutu a ranar Juma’a ba tare da sabanta dokar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.