Faransa-Macron

Faransa za ta ninka yawan jami'an tsaronta nan da shekaru 10

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar da shirin ninka yawan jami'an 'yan sanda da Jandarmomi kasar nan da shekaru 10. Macron ya bayyana haka ne cikin jawabi dangane da shirin tsaurara sa ido kan jami’an tsaron Faransa da ake zargi da cin zarafi da kuma nuna wariyar launi.

Jawabin shugaba Emmanuel Macron, yayin jawabinsa a kwalejin horar da 'yan sanda ta Faransa.
Jawabin shugaba Emmanuel Macron, yayin jawabinsa a kwalejin horar da 'yan sanda ta Faransa. Ludovic MARIN POOL/AFP
Talla

Da ya ke jawabi a babbar makarantar 'yan sanda da ke garin Roubaix, a arewacin Faransa, Macron ya ce zai kafa majalisa ta musamman mai alhakin sa ido kan halaye da ayyukan jami’an ‘yan sandan kasar.

Jawabin Macron ya biyo bayan tattaunawar da aka shafe watanni ana yi tsakanin masu ruwa da tsaki kan aikin ‘yan sanda da kuma dangantakar su da jama'a, biyo bayan bidiyon da ke nuna wasu ‘yan sanda fararen fata 4 suna lakadawa wani bakar fata dukan kawo wuka a dakinsa na shirya wakoki da ke birnin Paris a watan Nuwamban shekarar bara.

Cin zarafin da aka yi wa Michel Zecler ya fusata jama’a, ciki har da masu fafutukar kare hakkin dan adam na Black Lives Matter da ke Faransa, wadanda suka yi A-wadai da munanan dabarun da ‘yan sanda ke amfani da su kan marasa rinjaye, musamman maza bakar fata da Larabawa.

Daya daga cikin jerin soke-soken da aikin 'yan sanda ya dade yana fuskanta a Faransa, shi ne rashin wanzuwar wata hukuma mai zaman kanta da ke sa ido kan ake aiwatar da shi.

Hukumar IGPN wato “Inspection Generale de la Police Nationale, da a halin yanzu ke sauraron korafe -korafe, yawancin jami’an ta ‘yan sanda ne kuma ministan cikin gida, ke nada wanda zai jagorance ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI