Amurka

An gudanar da gangamin adawa da dokar hana zub da ciki a Amurka

Mata masu zanga zangar adawa da dokar hana zub da ciki a birnin Washington na Amurka
Mata masu zanga zangar adawa da dokar hana zub da ciki a birnin Washington na Amurka AP - Eric Kayne

Dauke da kwalayen da aka rubuta jikina, zabina, damata, dubban mata ne suka bazama titunan birnin Washington na Amurka a ranar farko na gangamin gama gari don nuna adawa da kokarin da masu ra’ayin mazan jiya ke yin a dkile damar zub da ciki.

Talla

Rikicin  ya yi kamari ne tun lokacin da jihar Texas ta bullo da dokar da ta haramta duk wani nau’i na zubar da ciki ne a ranar 1 ga watan Satumba, lamarin da ya sa masu rajin kare wannan damar suka garzaya kotu don  kalubalantar dokar.

Kwanaki 2 gabanin hukuncin kotun kolin kasar a game da wannan batu, kusan kungiyoyi 200 ne suka yi kira ga masu kare zub da ciki da su daga muryoyinsu don nuna adawa da dokar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI