Faransa-HRW

Kungiyar HRW ta zargi 'yan sandan Faransa da cin zarafin 'yan cirani

Wasu 'yan sandan Faransa.
Wasu 'yan sandan Faransa. Bertrand Guay AFP

Kungiyar kare hakkin dan adam ta human Rights Watch ta zargi ‘yan sandan Faransa da cin zarafin ‘yan ci rani da bakin haure a kasar, ta hanyar yi musu azaba, da kuma jefa rayuwar su cikin hadari.

Talla

Ta cikin wani rahoto da kungiyar ta fitar ya nuna yadda jami’an tsaron Faransa ke rushewa tare da yaga tantunan da ‘yan ciranin da suka kafa, su na gudanar da rayuwar su, abinda kuma ya ke tilasta musu garari ba tare da sanin ina suka dosa ba.

Ta cikin rahoton mai shafi 75, Human Rights Watch din ta kuma ce jami’an tsaron na Faransa na korar ‘yan ciranin daga wuraren da suka fake ta yadda su ke kamasu da laifin gararamba ba bisa ka’ida ba.

Kungiyar, ta kuma ce jami’an tsaron na amfani da karfin da ya wuce kima wajen tarwatsa ‘yan ciranin da ke Calais, abinda ke zuwa shekaru 5 bayan da suka tarwatsa mazaunin su da ke sansanin Jungle, abinda ya jefa rayuwar mutane sama da dubu 10 cikin hadari.

Calais dai guri ne da ya zama sansanin ’yan ci rani da ke shiga Faransa daga Africa da Asiya da kuma gabas ta tsakiya da nufin ratsawa turai zuwa Birtaniya tsawon shekaru.

Acewar rahoton na HRW matakin hana kwararar ‘yan cirani kwarara Faransa na cikin tsare-tsaren shugaban Faransa Emmanuel Macron, inda yanzu haka gwamnatinsa ta kaddamar da wani sabon gangami na hana ‘yan ci ranin shiga kasar, wanda kuma karkashin sa ne ‘yan sandan ke wannan aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI