Africa ta kudu

Drogba ya samu rauni a wasan sada zumunci

Jagoran Yan wasan kasar Cote d’ivoire, Didier Drogba
Jagoran Yan wasan kasar Cote d’ivoire, Didier Drogba REUTERS/Denis Balibouse

Jagoran Yan wasan kasar Cote d’ivoire, Didier Drogba, ya samu rauni a kafadar sa ta dama, a wasan sada zumuncin da sukayi da kasar Japan.Drogba ya samu raunin ne, a mintina 16 na farkon wasan, bayan yayi karo da Marcus Tanaka, Dan wasan baya na kasar Japan, abinda ya sa aka fidda shi daga wasan.Rahotanni sun ce, kafin raunin nasa, sai da Dan wasan dake wa kungiyar Chelsea wasa, ya jefa kwallo a raga.