Ferdinand ya fice taga tawagar England
Ferdinand ya fice taga tawagar England
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Jagorar Yan wasan Ingila, a gasar cin kofin duniya, da za’a fara a kasar Africa ta kudu, Rio Ferdinand, ya fice daga tawagar kasar, sakamakon raunin da ya samu a gwuiwa.Ferdinand ya samu rauni ne lokacin da suka hada kwanjin da Emile Heskey a wajen atisaye, kuma binciken likitoci ya nuna cewar, Ferdinand, ya samu raunin da zai hana shi shiga gasar da za’a fara makon gobe.Wannan ya baiwa Steven Gerrard, damar karbar ragamar jagorancin Yan wasan, yayin da aka gaiyato Michael Dawson, na kungiyar Tottenham, domin maye gurbinsa.