Kasashen Africa A Wasan Cin Kofin Kwallon Kafa Na Duniya

Sauti 09:58
Reuters

A tarihin Africa dai wannan ne karo na farko da nahiyar ta samu karbar bakuncin gasar Cin Kofin Kwallon Kafa na duniya. Wasan da za’a kwashe wata daya ana gudanarwa a kasar Africa ta Kudu daga 11 ga watan Yuni zuwa 11 ga watan Yulin shekarar 2010.Kasashe dai shida ne zasu wakilci Nahiyar da suka hada da kasar Africa ta kudu da kasar Algeria da kasar Kamaru da Ghana da kuma Nigeria. Abinda kuma ake tunanin daya daga cikinsu zai kafawa nahiyar tarihi na lashe gasar.Dangane da haka ne dai shirin Wasanni na Musamman na Rediyon Faransa yayi nazari kan irin rawar da wadannan kasashe zasu taka a wannan gasa karo na farko da za’a gudanar a nahiyar Africa.An dai tattauna da masana kwallon kafa tare da wasu daga cikin ‘yan wasan da zasu halarci wannan gasa.Kuma a shirin zaku ji alkwarin da Seff Blatter shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA ya dauka idan har kasashen suka nuna kwazo a gasar.