Africa ta kudu

An Harbi Wani Ba-Amirke

Tsohon Shugaban Afrika Ta Kusu Nelson Mandela Da Kofin Kwallo Na Dunita
Tsohon Shugaban Afrika Ta Kusu Nelson Mandela Da Kofin Kwallo Na Dunita ©AFP

Rahotanni daga kasar Afrika ta kudu na nuna cewa masu halartan gasan wasannin kwallon kafa na cin kofin duniya sun fara zaman zullumi sakamakon bindige wani Ba-Amirke da wasu da baa sani ba sukayi.Sai dai kuma masu shirya gasan wasannin na cewa ko kusa, babu wani dalili da zai sa hankulan jamaa ta tashi.A jiya ne dai wasu da ake kyautata zaton ‘yan fashi ne suka harbi Ba-Amirken da bindiga, alokacin da yake taka sayyada a birnin Johannesburg don neman Otel da zai sauka.Wata mai magana da yawun ‘yan sanda, Sally de Beer tace an kwashi mutumin zuwa asibiti, kuma wai  yace ba kallon kwallo ne ya kaishi kasar Afrika ta kudu ba.Jamian ‘Yan sandan tace harsashin ya makale akafadar mutumin, kuma anyi katarin cirewa, har mutumin na samun sauki a Asibiti.Dama, ana fargaban aukuwan irin haka a wannan kasa da ake gudanar da gasan wasannin kwallon kafa na cin kofin duniya, inda ake ganin tana sahun gaba wajen laifuka a duniya