Isa ga babban shafi
Indiya

An dakatar da ‘Yan wasa 7 zuwa commonwealth a Indiya

shirin wasannin commonwealth a indiya
shirin wasannin commonwealth a indiya
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 1

Hukumar yaki da miyagun kwayu a kasar Indiya ta dakatar da wasu ‘Yan wasa bakwai daga zuwa wasannin renon Ingila na Commonwealth da za’a gudanar a New Delhi bayan wani gwaji da aka gudanar da ya shafi lafiyarsu.‘yan wasan dai sun hada da ‘yan dambe hudu da masu wasan iyon ruwa guda biyu da kuma daya daga cikin masu wurga karfe.Masu iyon ruwa da suka kasance mata Richa Mishra da kuma Jyotsna Pansare bayan gudanar da gwajin an gano suna da matsalar daya shafi toshewar nunfashi hadi da kuma ‘yan damben guda hudu Rajiv Tomar da Sumit Kumar da Mausam Khatri da kuma mace daga cikinsu Gursharanpreet Kaur.  

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.