Indiya

Dan Indiya Ya Lashe Zinari Wajen Harbin Bindiga

Irin Bindigan da akayi gasan harbin da ita
Irin Bindigan da akayi gasan harbin da ita RFI Hausa

Wani gwanin iya harbi da bindiga dan kasar Indiya ya lashe lamban zinari, wajen iya harbi da bindiga, a cigaba da gasan wasannin motsa jiki na kasashe renon Ingila da akeyi a New Delhi na kasar Indiya.Mutumin mai suna Omkar Singh ya kasance shine gwanin iya harbin bindiga da maza sukayi na mita 50.A yau ne dai akayi wannan gasa na harbin bindiga na maza.