Manchester

Rooney ya amince da sabuwar yarjejeniya da Manchester

Wayne Rooney, dan wasan Manchester United.
Wayne Rooney, dan wasan Manchester United. Reuters

Dan wasan Manchester United Wayne Rooney ya janye matakin da ya dauka na barin Old Trafford bayan da a yau Juma’a ya sanya hannu ga sabuwar yarjejeniyar shekaru biyar da kungiyar kwallon kafar.A ranar laraba ne da ta gabata Wayne Rooney ya girgiza Manchester inda yace zai bar kungiar kwallon kafar saboda wasu dalilai daya danganta cewa Manchester ta gaza sayo sabbin ‘yan wasa da zai bata damar kece raini.Sai gashi kuma a yau juma’a a shafin yanar gizon kungiyar kwallon kafar an bayyana cewa Wayne Rooney ya amince da sabuwar yarjejeniyar shekaru biyar da kungiyar kwallon kafarKodayake dan wasan ya bayyana cewa mai horar da ‘yan wasan kwallon kafar Manchester Sir Alex Faguson ne ya tursasa masa amincewa da sabuwar yarjejeniyarkamar yadda kuma mai horar da ‘yan wasan Arsenal Arsene Wenger ya bayyana cewa, ya yi mamakin yadda Rooney ya amince da sabuwar yarjejeniyar da Manchester United.