FIFA

Amirka da Japan Basu Gamsu Da Zaben FIFA Ba

Shugaban FIFA, Joseph Blatter yana bayyana sakamakon zaben
Shugaban FIFA, Joseph Blatter yana bayyana sakamakon zaben rfi

Kasashen da basu yi nasaran samun daukan nauyin gasan wasannin kwallon kafa na cin kofin duniya ba, da aka bada sanarwa jiya, sun nuna rashin goyon bayan su gameda matakan da Hukumar FIFA ta dauka.Jiya Hukumar Gasan wasannin kwallon kafan ta duniya FIFA ta zabi kasar Russia da Qatar domin daukan nauyin gasan wasannin kwallon kafa na duniya na shekara ta 2018 da 2022.Shugaban kasar Amirka Barack Obama ya bayyana zaben da cewa kuskure ne, kasancewar kasar Amirka ta rasa inda aka baiwa Qatar amincewa.Shima mataimakin Shugaban Hukumar Wasanni na kasar Japan Kuniya Daini ya nuna baa kyauta masu ba.Kasar Amirka, Qatar, Japan,Korea ta kudu da Australia sun bayyana niyyar su ta daukan nauyin gasan wasannin kwallon kafa na cin kofin duniya cikin shekara ta 2022.