Argentina

Argentina Zata Buga Kwallo da Portugal Da Amirka

Mai horas da 'yan wasan kasar Argentina Diego Armando Maradona
Mai horas da 'yan wasan kasar Argentina Diego Armando Maradona rfi

Kasar Argentina zata kara da kasar Portugal a wasan kwallon kafa na sada zumunci da zasuyi ranar 9 ga wannan watan a London.Shugabannin Hukumar Kwallon kafan kasar Argentina suka bada sanarwan wannan wasa.Kasar Argentina ta shirya zatayi wasannin kwallon kafa da Amirka wanar 26 ga watan uku na sabon shekara a Seattle, sannan kuma ta kara da Costa Rica ranar 29 ga watan uku na sabuwar shekara mai kamawa a San Jose.