Chelsea

Drogba zai Buga Wasan Gobe

Dan wasan Chelsea Didier Drogba
Dan wasan Chelsea Didier Drogba RFI

Didier Drogba gwanin wasan kwallon kafa na Klob din Chelsea na shirin komawa fagen wasa gobe, a wasan da zasu buga da Klob din Olympique Marseille.Drogba zai jagoranci ‘yan wasan Klob din nasa, kodashike Nicolas Anelka da Ashley Cole ba zasu buga wasan ba.Drogba ya taba bugawa Marseille har suka kai ga nasara cikin shekara ta 2004, kafin ya koma Club din Chelsea.