Wassani a yau yadda su ka kassance
Wallafawa ranar:
Steven Taylor ya sake radaba hannu kan wani sabon kwantaragi da kungiyar kwallon kaffa ta Newcastle.Wanan sabuwar kwangillar za ta bashi dama cigaba da taba leda har zuwa shekara ta 2016 a cikin kungiyar.A gasar cin koffin kwallo na Najeriya a kwanaki na 8,a yanzu dai Sunshine na kan gabada maki 16.Dolphin FC na bayanta da maki 15.Kano Pillllars na Pili ita ma da maki 13 .Bayan da aka kare wassar kokowar galgajiya jiya a birnin Tillaberi na jumhuriyar Nijar,gwamnan jahar sokoto a tarrayar Najeriya Aliyu Magatakardan wamako ,ya kasance wanda ya samu takobi daga cikin gwabnonin Najeriya, game da halartashi a wassani kokowar galgajiya ta fanin tsagwaron sada zumunta tsakanin al’ummomin 2.A wassar kwondo a yankin arewacin Amurika,karo da ya ka gudana a karshen wanan sati :La Clippers da Phoenix 108-103Minnesota-Cleveland 98 -97Chicago-Detroit 95-92 A kasar Kamaru game da cinkoffin zakaru na kasar ,kungiyar Coton Sport ta Garoua na kan gaba da maki 16 .Canon de Yaounde da maki 12.Universite Ngaoundere 12Unisport Bafang na da maki 11.